‌Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari

‌Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayi mana wata huɗuba ba sai ya ce: «‌Babu imani ga wanda ba shi da amana, kuma babu Addini ga wanda ba shi da alƙawari».

[Hasan ne ta wani Sanadin] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Anas ɗan malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa da wahala Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi huɗuba ko ya yi wa'azi sai ya ambaci al'amura biyu: Na farko: Babu imani cikakke ga wanda a ransa akwai ha'inci ga wani mutum a cikin dukiyarsa ko ransa ko kuma iyalansa. Na biyu: Babu Addini cikakke ga wanda yake ha'intar alƙawurra kuma yake warwaresu.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan mayar da amana da kuma cika alƙawari, domin warwaresu yana tauye imani.

Gargaɗarwa akan ha'intar amana da kuma warware alƙawari, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.

Hadisin ya ƙunshi kiyaye amana da kuma alƙawarin da ke tsakanin Allah da bawanSa, da kuma wanda ke tsakanin halitta sashinsu da sashi.

التصنيفات

Kyawawan Halaye