إعدادات العرض
Kada ka yi fushi
Kada ka yi fushi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili فارسی မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands සිංහල தமிழ் ไทย دری Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių or Română Kinyarwanda Српски O‘zbek Moore नेपाली Malagasy тоҷикӣ Oromoo Wolof Soomaali Български Українська Azərbaycan ქართული bm Македонскиالشرح
Ɗaya daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - ya nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da shi a kan wani abin da zai amfaneshi, sai ya umarceshi da kada ya yi fushi, ma'anar hakan cewa shi ne ya nisanci sabubban da za su sa shi fushi, kuma ya tsare kansa idan fushi ya faru gareshi, kada ya zarce tare da fushinsa da kisa ko duka ko zagi da makamancin hakan. Mutumin ya maimaita neman wasiyya da yawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai ƙara komai a wasiyyarsa ba a kan "Kada ka yi fushi".فوائد الحديث
Gargaɗi daga fushi da sabubbansa, domin cewa shine matattarar sharri, kiyayarsa shi ne matattarar alheri.
Yin fushi saboda Allah; kamar fushi a lokacin keta alfarmomin Allah ya na daga fushi abin yabo.
Maimaita zance a lokacin buƙata har mai ji ya kiyayeshi ya riski muhimmancinsa.
Falalar neman wasiyya daga malami.
التصنيفات
Kyawawan Halaye