Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku…

Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa musulmi, kowane musulmi akan musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa musulmi wasiyya ta alheri ga ɗan'uwansa musulmi, kuma ya bayyana sashin abinda yake wajaba akansa na wajibai da ladubba daura da su; daga hakan: Wasiyya ta farko: Kada ku yi wa juna hassada, ita ce sashinku ya yi burin gushewar ni'imar sashi. Na biyu: Kada ku yi cinikin koɗe shi ne mutumin da ba ya nufin yin siyan abin siyan sai ya yi ƙari a farashin abin siyan; kawai yana nufin anfanar mai siyarwar, ko cutar da mai siyan. Na uku: Kada ku yi ƙiyayya, ita ce nufin shigar da cuta kuma ita ce kishiyar soyayya; sai dai idan ƙiyayyar ta kasance ne a lamarin Allah ne - Maɗaukakin sarki -; to shi wajibi ce. Na huɗu: Kada ku juyawa juna baya, shi ne kowane ɗaya daga cikinku ya juyawa ɗan'uwansa bayansa da ƙeyarsa sai ya bijire masa kuma ya ƙaurace masa. Na biyar: Kada sashinku ya yi ciniki akan cinikin sashi, shi ne yacewa mai siyan: A wurina akwai irinta da ƙasa da farashinta ko ta fita kyau kuma farashinta bai kai nata ba. Sannan tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi wasiyya da wasiyya mai tattaro (ma'anoni da hikimomi masu yawa) sai ya ce: Ku zama kamar 'yan'uwa ta hanyar barin abubuwan da aka hana, da kuma nuna soyayya da sassauci da tausayi da sauƙaƙawa da taimakekeniya a aikin alheri, tare da tsarkakakkiyar zuciya da kuma yin nasiha a kowane hali. Daga abinda wannan 'yan uwantakar take hukuntawa: Kada ya zalinci ɗan'uwansa musulmi kuma ya yi ta'addanci akansa. Kada ya bari a zalinci ɗan'uwansa sai ya ƙi taimakonsa a gurin da yake da ikon ya taimake shi, kuma ya ɗauke masa zalincin. Kuma kada ya wulaƙanta shi ya raina shi ya dinga kallonsa da kallo na raini da izgili; shi mai fitowa ne daga girman kai a cikin zuciya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana har sau uku cewa tsoron Allah a cikin zuciya yake, wanda a cikin zuciyarsa akwai tsoron Allah wanda yake hukunta kyakkyawar ɗabi'a, da tsoron Allah da muraƙabarSa to cewa shi ba zai wulaƙanta musulmi ba, kuma ya ishe shi ɗabi'u na sharri da ƙasƙanci ya wulaƙanta ɗan'uwansa musulmi, hakan saboda girmankan dake cikin zuciyarsa. Ya Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa kan abinda ya wuce cewa kowane musulmi akan musulmi haramun ne: jininsa: Shi ne ya yi masa ta'addanci da kisa ko abinda bai kai kisa ba kamar rauni ko duka da makamancinsu, haka nan dukiyarsa: Shi ne ya ci dukiyar ba tare da wani haƙƙi ba, haka nan mutuncinsa: Shi ne ya zarge shi a kansa ko tsareshi.

فوائد الحديث

Umarni da dukkan abinda 'yan uwantaka ta imani take hukunta wa, da kuma hani daga binda yake kishiyantarta na maganganu da ayyuka.

Madogarar tsoron Allah ita ce abinda ke cikin zuciya na sanin Allah, da tsoronSa da muraƙabarSa, kuma wannan taƙawar taba fitowa ne daga ayyuka na gari.

Kaucewa ta zahiri tana nuni akan raunin taƙawa ta zuciya.

Hani daga cutar da musulmi ta kowace fuska daga fuskoki na magana ne ko aiki.

Ba hassada ba ne musulmi ya yi burin ya zama tamkar waninsa, ba tare da burin gushewar (ni'ima ba) daga wani, wannan ana kiransa kishi; kuma wannan ya halatta yana taimako akan rigegeniya zuwa ayyukan alheri.

A ɗabi'ar mutum yana ƙin ace wani ya fishi a wani abu na falaloli, to idan ya so gushewarta daga ɗayan to wannan ita ce hassada, idan kuma ya so rigegeniya to wannan shi ne kishin da ya halatta.

Idan ya bayyanawa mai siye cewa mai siyarwar ya ha'ince shi ha'inci mai muni a cikin siyansa to wannan ba ya cikin cinikin musulmi akan cinikin ɗan'uwansa; kai wannan yana daga mahukuntar nasiha, amma da sharaɗin niyyarsa ta zama ita ce yi wa ɗan'uwansa mai siye nasiha ba wai cutar da mai siyarwar ba, ayyuka kuwa (ana musu hukunci ne) da niyyoyi.

Idan musu cinikin ba su yarda da cinikin ba kuma farashin bai tabbata ba to hakan ba ya daga cikin ciniki akan cinikin ɗan'uwansa.

Kiyayya saboda Allah ba ta cikin ƙiyayyar da aka yi hani a kanta a cikin hadisin, kai shi wajibi ne ma, kuma yana daga mafi amintakar igiyar imani.

التصنيفات

Kyawawan Halaye, Tsarkake Zuciyoyi