‌Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarwa akan tausasawa abinda ba Ya bayarwa akan tsanantawa, da kuma abinda ba Ya bayarwa ga waninsa

‌Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarwa akan tausasawa abinda ba Ya bayarwa akan tsanantawa, da kuma abinda ba Ya bayarwa ga waninsa

Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Ya ke Aisha lallai Allah Mai tausasawa ne kuma Yana son tausasawa, Yana bayarwa akan tausasawa abinda ba Ya bayarwa akan tsanantawa, da kuma abinda ba Ya bayarwa ga waninsa».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitawa uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - sauƙi, kuma Allah Mai sauƙi ne Mai sauƙaƙawa bayinSa ne, yana son sauƙi garesu ba Ya so musu tsanani, dan haka ba Ya ɗora musu abinda yafi ƙarfinsu, kuma Yana son bawanSa ya siffantu da tausayi a lamura da kuma riƙo da sauƙi; kada ya zama mai kaushin zuciya mai tsanantawa, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - a duniya Yana bada kyakkyawan yabo da samun abin nema da sauƙaƙa abin nufi saboda sauƙi da tausasawa, a lahira kuma Yana bada gwaggwaɓan lada, sama da yadda Yake bayarwa akan tsanani da kausasawa, sauƙi yana zuwa tare da abinda waninsa ba ya zuwa tare da shi.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan sauƙaƙawa da kuma hani akan tsanani.

Ɗaukakar matsayin sauƙi tsakanin kyawawan ɗabi'u.

Mai sauƙaƙawa yana cancantar kyakkyawan yabo da kuma gwaggwaɓan lada daga Allah - Maɗaukakin sarki -.

Sindi ya ce: Tsanani kishiyar sauƙi ne, wato wanda yake kiran mutane zuwa ga shiriya da sauƙi da kuma tausasawa ya fi alheri daga wanda yake kiran mutane da tsanani idan bigiren ya kasance yana iya karɓar al'amura biyun, inba haka ba to abinda bigiren yake iya karɓarsa shi ne zai ayyana, Allah ne Mafi sani da haƙiƙanin hali.

التصنيفات

Kyawawan Halaye