إعدادات العرض
Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa
Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල አማርኛ অসমীয়া Kiswahili Tiếng Việt ગુજરાતી Nederlands پښتو नेपाली ไทย മലയാളം Svenska Кыргызча Română Malagasy ಕನ್ನಡ Српски తెలుగుالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.فوائد الحديث
Wajabcin so wa mutum ga ɗan'uwansa abinda yake so wa kansa; domin kore imani ga wanda ba ya son abinda yake so ga ɗan'uwansa yana nuni akan wajabcin hakan.
'Yan uwantaka a tafarkin Allah sama take akan 'yan uwantaka ta nasaba, to hakkinta shi ne mafi wajaba.
Haramcin dukkan abinda yake kore wannan soyayyar na maganganu da ayyuka, kamar algus da raɗa da hassada da ta'addanci akan ran musulmi ko dukiyarsa ko mutuncinsa.
Yin anfani da wasu daga lafuzza masu kwaɗaitarwa akan yin aiki; saboda faɗinsa: "Ga ɗan'uwansa".
Karmani - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Kuma yana daga cikin imani ya ki wa ɗan'uwansa abinda yake ki wa kansa na sharri, amma bai ambace shi ba; domin son abu mai lazimtar kin kishiyarsa ne , to hakan ya isu akan barin fadinsa.
التصنيفات
Kyawawan Halaye