Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama

Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wani musulmi ba zai suturta ɗan uwansa musulmi ba a cikin wani al'amari daga al'amura, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya suturta shi a ranar alƙiyama; sakayya tana daga jinsin aiki, kuma suturcewar Allah gare shi zai zama da suturcewar laifukansa da saɓonsa daga yaɗasu ga ma'abota taron alƙiyama, zai iya kasancewa da barin yi masa hisabi akansu da kuma anbata masa su.

فوائد الحديث

Halaccin rufawa musulmi asiri idan ya aikata wani saɓo, tare da yin inkari akansa da kuma yi masa nasiha, da tsoratar da shi Allah, amma idan ya kasance daga ma'abota sharri da ɓarna ne masu bayyana saɓo da fasiƙanci, to cewa shi ba ya kamata a rufa musu asiri; domin rufa musu asiri zai sa su ƙarfin hali akan saɓo, kawai ana ɗaga al'amarinsa ne zuwa ga hukuma, koda a hakan akwai anbatansa; domin cewa shi mai bayyanar da fasiƙancinsa ne da kuma saɓonsa.

Kwaɗaitarwa a kan rufa asirin kurakuren wasu.

Daga fa'idojin rufa asiri: Bada dama ga mai yin zunubi ya yi tinani kuma ya tuba zuwa ga Allah; domin bayyanar da aibuka da al'aurori yana daga yayata alfasha, kuma yana ɓata yanayin zamantakewa, kuma yana ruɗar mutane da aikata su.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Kyawawan Halaye