Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba

Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba

Daga Jariri ɗan Abbdullah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda baya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba, to, jin ƙan bawa ga halitta yana daga mafi girman sabubban da ake samun rahamar Allah da su.

فوائد الحديث

Jin ƙai abin nema ne ga sauran ababen halitta, sai dai an keɓanci mutane da ambato ne don ba da muhimmanci garesu.

Allah Shi ne Mai jin ƙai, kuma Yana jin ƙan bayinsa masu jin ƙai, to, sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki.

Jin ƙai ga mutane ya tattaro alheri garesu da tunkuɗe sharri garesu da mu'amalantarsu da kykkyawa.

التصنيفات

Kyawawan Halaye