Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba

Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba".

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bai zamo daga sha'anin mumimi mai cikakken imani ya zama mai yawan aibata mutane a cikin dangantakar su ba, kuma ba mai yawan zagi da tsinuwa bane, kuma ba mai yawan alfasha ne da aiki ko magana wacce babu kunya a cikinta ba.

فوائد الحديث

Kore imani a cikin nassosin shari'a ba ya kasancewa sai dan aikata wani aiki na haramun ko barin wajibi.

Kwaɗaitarwa akan kiyaye gaɓɓai da kiyayesu daga munanan abubuwa, musamman ma harshe.

Assindi ya ce: A cikin sigar mubalaga a cikin (mai yawan suka, da mai yawan tsinuwa) akwai nuni akan cewa idan suka da tsinuwa sun zama kadan ne ga wanda yake cancantar hakan ba ya cutarwa a cikin siffantuwa da siffofin ma'abota imani.

التصنيفات

Kyawawan Halaye, Ladaban Magana da kuma shiru