Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne

Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne, waɗanda suke adalci a hukuncinsu da iyalansu da abin da suka jiɓinta".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa waɗanda suke hukunci da adalci da gaskiya a tsakanin mutane waɗanda suke ƙarƙashin shugabancinsu da hukuncinsu da iyalansu, cewa su za su zauna a kan abubuwan zama maɗaukaka haƙiƙa an haliccesu daga haske, don girmamawa garesu a ranar al-ƙiyama. Waɗannan munbarorin suna daman Ubangiji Al-Rahman, kuma su duka hannayensa biyun na dama ne.

فوائد الحديث

Falalar adalci da kwaɗaitarwa a kansa.

Adalci mai gamewa ne ya tattaro dukkanin shugabanci da hukunci a tsakanin mutane, har adalci a tsakanin ma'aurata da 'ya'ya da sauransu.

Bayanin matsayin masu adalci a ranar al-ƙiyama.

Banbance-banbancen matsayiyyikan ma'abota imani a ranar al-ƙiyama kowanne da gwargwadon aikinsa.

Salon kwaɗaitarwa yana daga salon kiran da zai kwaɗaitar da wanda ake kira a aikin ɗa'a.

التصنيفات

Kyawawan Halaye