Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska

Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni: "Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya kwaɗaitar a kan aikin alheri, kuma kada ya wulaƙantashi ko da ya kasance kaɗan ne, daga wannan (akwai) sakin fuska ta hanyar murmushi a yayin haɗuwa, to, yana kamata ga musulmi ya yi kwaɗayi a kansa; saboda abin da ke cikinsa na ɗebe kewa ga ɗan uwa musulmi da shigar da farin ciki gareshi.

فوائد الحديث

Falalar soyayya a tsakanin muminai da murmushi da walwala a yayin haɗuwa.

Cikar wannan shari'ar da tattarowarta, kuma ita ta zo da dukkanin abin da a cikinsa akwai gyara musulmai da haɗe kansu.

Kwaɗaitarwa a kan aikata aikin alheri ko da ya ƙaranta.

An so shigar da farin ciki ga musulmai; saboda abin da ke cikin hakan na tabbatar da sabo a tsakaninsu.

التصنيفات

Kyawawan Halaye