An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u

An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".

[Hasan ne kuma Ingantacce]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - yana bayyana cewa mafi giman sabubban da suke shigar da mutane aljanna sabubba biyu ne, sune: Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u. Tsoron Allah: Shi ne ka sanya kariya tsakaninka da tsakanin azabar Allah, ta hanyar aikata umarninsa da nisantar hane-hanensa. Kyakkyawar ɗabi'a: Tana kasancewa ne da shinfiɗar fuska, da yin aikin kirki, da kamewa daga cuta. Kuma mafi girman sabubban da suke shigarwa wuta sabubba biyu ne, su ne: Harshe da farji. yana daga saɓon harshe: Ƙarya, da raɗa, da annamimanci da wasunsu. Yana daga saɓon farji: Zina da luwaɗi da wasunsu.

فوائد الحديث

Shiga aljanna yana da sabubban da suka rataya da Allah - Maɗaukakin sarki, daga cikinsu akwai: Tsoronsa, da kuma sabubban da suke rataya da mutane, daga cikinsu akwai: Kyawawan ɗabi'u.

Hatsarin harshe ga mai shi, kuma yana daga sabubban shiga wuta.

Hatsarin sha'awe-sha'awe da ayyukan alfasha ga mutum, kuma suna daga mafi yawan sabubban shiga wuta.

التصنيفات

Kyawawan Halaye, Sifar Al-janna da Wuta