Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu)

Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu)

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu), sai ya gamu da Allah sai Ya yafe masa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Game da mutumin da ya kasance yana mu'amalar bashi tare da mutane, ko ya siyar bashi, Ya kasance yana cewa yaronsa wanda yake karbo masa basukan dake hannun mutane: Idan ka je wurin wanda ake bi bashi kuma ba shi da abinda zai biya bashin dake kansa dan gajiyawarsa "To ka kau da kai gare shi"; ko dai da jinkirta masa da rashin nace masa a kan ya biya., Ko da karbar abinda ke tare da shi koda tare da abinda ke cikinsa ne na tawaya, hakan dan kwadayi daga gare shi akan Allah Ya ketare masa kuma ya yi masa rangwame. Lokacin da ya mutu sai Allah ya yi masa afuwa kuma ya ketare daga munanan ayyukansa.

فوائد الحديث

Kyautatawa a cikin mu'amalantar mutane da afuwa daga garesu da ketarewa daga wanda ke cikin mawuyacin hali a cikinsu yana daga mafi girman sabubban tsiran bawa a ranar Alkiyama.

Kyautatawawa halitta da tsarkakewa sabo da Allah da kwadayi a rahamarSa yana daga sabubban gafarar zunubai.

التصنيفات

Kyawawan Halaye