Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi

Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa ƙarfi na haƙiƙa ba ƙarfin jiki ba ne, ko wanda yake ka da wasu ƙarfafa, kaɗai mai tsananin ƙarfi shi ne wanda yake yaƙar zuciyarsa, kuma yake rinjayarta a lokacin da fushi ya yi tsanani a gareshi; domin cewa wannan yana nuni a kan ƙarfin da zai tabbatar da shi a kan kansa da rinjayarsa a kan Shaiɗan.

فوائد الحديث

Falalar haƙuri da kiyaye rai a lokacin fushi, kuma cewa yana daga cikin ayyuka na gari waɗanda musulunci ya kwaɗaitar a kansu.

Yaƙar zuciya a lokacin fushi shi ne mafi tsanani daga yaƙar maƙiyi.

Canjawar musulunci ga fahimtar ƙarfi irin na Jahiliyya zuwa ɗabi'u masu girma, to, mafi tsananin mutane a karfi shi ne wanda ya mallaki ragamar kansa.

Nisanta daga fushi; saboda abin da yake jawowa na cutarwa a kan ɗaiɗaiku da jama'a.

التصنيفات

Kyawawan Halaye