Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana

Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana

Daga Abu Darda - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi nauyin abinda ke ma'aunin mumini ranar Alkiyama na ayyuka da maganganu shi ne kyawawan dabi'u, hakan ta hanyar sakin fuska, da barin cutarwa, da yin alheri. Allah - Madaukakin sarki - Yana kin mai munanawa a aikinsa da maganarsa, mai munanawa a abinda harshensa yake furtawa da shi.

فوائد الحديث

Falalar kyawawan dabi'u; domin cewa shi yana gadar da soyayyar Allah ga mai shi, da kuma soyayyar bayin Allah, shi ne mafi girman abinda ake aunawa a ranar Alkiyama.

التصنيفات

Kyawawan Halaye, Ladaban Magana da kuma shiru