إعدادات العرض
Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora
Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands Kiswahili தமிழ் دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Soomaali Moore Українська Български Wolof Azərbaycan ქართული тоҷикӣ bm Oromoo Македонскиالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da umarnin sauƙaƙawa da rangwame wa mutane, da kada a tsananta musu a dukkanin lamura na addini da na rayuwa, wannan kuwa a daidai yadda Allah Ya halatta Ya kuma shar’anta. Kuma yana kwaɗaitarwa a kan bushara da alheri, da rashin korar (kyarar) mutane.فوائد الحديث
Wajibin dake kan mumini shi ne ya sanya wa mutane son Allah, ya kwadaitar da su alheri.
Ya kamata ga mai kiran mutane zuwa ga Allah ya yi nazari cikin hikima a kan yadda zai isar da saƙon Musulunci zuwa ga mutane.
Bushara tana haifar da farin ciki da karɓuwa da nutsuwa da abin da mai Da'awa ya ke gabatarwa ga mutane.
Tsanantawa tana haifar da ƙyama da kuma juya baya da sanya shakku a maganar mai Da’awah.
Yalwatuwar rahamar Allah ga bayinSa, da cewa Ya yardar musu da addini mai sauƙi da Shari’ah mai rangwame.
Sauƙi da aka yi umarni da shi, shi ne wanda Shari’a ta zo da shi.
التصنيفات
Kyawawan Halaye