إعدادات العرض
Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna
Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne. Kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Português தமிழ் አማርኛ অসমীয়া Kiswahili ગુજરાતી Nederlands پښتو नेपाली മലയാളം Svenska ไทย Кыргызча Română Malagasy ಕನ್ನಡ Српски తెలుగు ქართული Moore Magyar Македонскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da gaskiya, kuma ya bada labarin cewa lazimtarta yana kaiwa zuwa aiki na gari madawwami, mai lazimtar aikin alheri yana kai mai shi zuwa ga aljanna, ba zai gushe ba gaskiya tana mai maituwa ga reshi a boye da fili, kuma yana cancantar sunan mai yawan gaskiya; shi ne kai matuƙa a gaskiya, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tsawatar daga ƙarya da faɗar ƙarya; domin cewa ita tana kaiwa zuwa karkacewa daga daidai da kuma aikin sharri da ɓarna da saɓo, sannan ta kaishi zuwa wuta, ba zai gusheba yana yawaita ƙarya har sai an rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah.فوائد الحديث
Gaskiya ɗabi'a ce mai girma tana samuwa ne ta hanyar aiki da ƙoƙari, domin cewa mutum ba zai gusheba yana gaskiya kuma yana kardadon gaskiya, har sai gaskiya ta zama ɗabi'a gare shi, sai a rubuta shi a wurin Allah cikin masu yawan gaskiya kuma mutanen kirki.
Ƙarya ɗabi'a ce abar zargi mai ita yana samuntane saboda tsawon gogayyarsa, da kardadonsa a faɗa da aikatawa, har sai ta wayi gari ɗabi'a, sannan a rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Gaskiya ana fadinta ne akan gaskiyar harshe, ita ce kishiyar ƙarya, da gaskiya a niyya ita ce ikhlasi, da gaskiya a ƙudirin niyya akan alheri da ya yi niyyarsa, da gaskiya a cikin ayyuka, mafi ƙarancinta daidaituwar zahirinsa da badininsa.
Da gaskiya a matakai, kamar gaskiya a tsoro da ƙauna da wasunsu, wanda ya siffantu da hakan to ya zama mai yawan gaskiya, ko (ya siffantu) da wasu daga cikinsu to ya zama mai gaskiya.
التصنيفات
Kyawawan Halaye