Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku

Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku

Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Mummunar magana ko mummunan aiki ba su kasance cikin dabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, bai nufe shi ba, kuma bai ganganta yinsa ba, to, shi fa [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ma’abocin ɗabi’u ne masu girma. Kuma [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: Lalle mafi falalarku a wurin Allah mafi kyawunku kyawawan ɗabi’u, ta hanyar bayar da abu mai kyau, da sakin fuska, da kamewa daga cutarwa, da juriya, da hulɗa da mutane da abu mai kyau.

فوائد الحديث

Ya wajaba ga mumini ya yi nesa da mummunar magana da kuma mummunan aiki.

Cikar ɗabi’un Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba abin da yake zuwa daga gare shi sai kyakkyawan aiki da daddaɗan zance.

Kyawawan ɗabi’u wani fage ne da ake rige - rige, duk wanda ya Riga, ya kasance zababbe cikin muminai kuma mafi cikar imaninsu.

التصنيفات

Kyawawan Halaye