Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba

Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ba ya godewa mutane to ba zai godewa Allah ba".

[Ingantacce ne] [رواه أبو داود والترمذي وأحمد]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda a al'adarsa ba ya godewa mutane akan alheri da abu mai kyau da suka yi masa to ba zai godewa Allah ba, hakan dan haduwar al'amura biyun da ɗaya, domin wanda daga cikin ɗabi'arsa da al'adarsa ita ce butulcewa ni'imar mutane da barin gode musu, to al'adarsa zata zama butulcewa ni'imar Allah da kuma kasawa a gode maSa.

فوائد الحديث

Muhimmancin godewa mutane akan aikin laheri.

Mai ni'imtarwa a haƙiƙa shine Allah - Maɗaukakin sarki -, ɗabi'u sabubba ne waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake horesu ga wanda Yake so, saboda haka ne lallai cewa godewa mutane yana daga cikin gode wa Allah - Maɗaukakin sarki -.

Godewa mutane akan aikin alherinsu dalili ne akan cikar ɗabi'u.

التصنيفات

Kyawawan Halaye