إعدادات العرض
Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa
Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa
Daga Sa’ad Ɗan Abu Waƙƙas, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Português മലയാളം తెలుగు မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Kiswahili தமிழ் دری Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Wolof Soomaali Moore Українська Български Azərbaycan ქართული тоҷикӣ bm Oromoo Македонскиالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa Allah mabuwayi Yana son wasu daga cikin bayinsa. Daga cikinsu akwai: Mai tsoron Allah wanda yake aikata abin da aka yi umarni, yake kuma nisantar hani. Kuma yana son: Wanda ya wadatu ga barin mutane, ya yi riƙo da Allah maɗaukaki, ba ya waigawa ga wanin Allah. Kuma yana son: Mai ɓoye kansa (wanda ba ya neman suna), mai tawalu’u, mai bauta ga Ubangijinsa, wanda ya shagaltu da abin da zai amfane shi, wanda bai damu da wani ya sanshi ba, ko wani ya yabe shi ba, ko ya burge ba.فوائد الحديث
Bayanin wasu siffofi masu sanyawa a samu son Allah ga bayinsa, wadanda suke su ne, Taƙ'wa da Tawalu’u da kuma yarda da abin da Allah ya raba.
التصنيفات
Kyawawan Halaye