:

Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «‌Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Munzir ibnu A'iz ga mai tabo a fuskar nan na ƙabilar Abdulƙais kuma shugabanta - Allah Ya yarda da shi - Lallai kai kana da siffofi biyu Allah Yana sonsu, sune: Hankali, da kuma tabbata da nutsuwa da kuma rashin gaggawa.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da haƙuri da kuma dangana.

Kwaɗaitarwa akan tabbata a cikin al'amura da kuma duba ƙarshensu.

Haƙuri da dangana suna daga cikin siffofi ababen yabo.

Mutum ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - akan abinda Ya halicce shi akansa na ɗabi'u ababen yabo.

Kalmar al-Ashaj ita ce wanda aka jiwa rauni a fuska, ko a kai, ko goshi.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Kyawawan Halaye