Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa

Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa

Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana daya daga sabubban da suke karfafa alaka tsakanin muminai kuma suke yada soyayya a tsakaninsu, shi ne cewa idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana son sa.

فوائد الحديث

Falalar tsarkakakkiyar soyayya saboda Allah - Madaukakin sarki - ba dan maslaha ta duniya ba.

Anso sanadar da wanda ake so sabo da Allah da soyayyrsa, dan soyayya da kauna su karu.

Yada soyayya tsakanin muminai yana karfafa 'yan uwantaka ta imani, kuma yana kiyaye zamantakewa daga rarrabuwa.

التصنيفات

Kyawawan Halaye, Ladaban Magana da kuma shiru