إعدادات العرض
Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa
Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.
[Hasan ne]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands සිංහල Kiswahili தமிழ் دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Wolof Soomaali Moore Українська Български Azərbaycan ქართული тоҷикӣ bm Oromooالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin mafi cikar imani a cikin mutane shi ne wanda ɗabi’unsa suka kyautata, ta hanyar sakin fuska, da bayar da abu mai kyau, da kyakkyawar magana, da barin cutarwa. Mafi alherin muminai shi ne mafi alherinsu ga iyalansa, kamar matarsa da ‘ya'yansa mata, da ‘yan’uwansa mata, da danginsa mata, domin su ne suka fi kowa haƙƙin a kyautata musu.فوائد الحديث
Falalar kyawawan dabi’u da cewar suna cikin imani.
Aiki yana cikin imani, shi kuma imani yana ƙaruwa yana raguwa.
Musulunci ya darajta mace, ya kwaɗaitar a kan kyautata musu.