Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu

Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu

Daga Shaddadu ɗan Aws - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Abubuwa guda biyu na haddacesu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu, idan za ku yi kisa, to, ku kyautata kisan, kuma idan za ku yi yanka, to, ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa, ya hutar da abin yankansa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawa a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.

فوائد الحديث

Rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarsa ga halitta.

Kyautata kisa da yanka: shi ne ya kasance ta fuskar da shari'a ta halatta.

Cikar shari'a da tattaruwarta a kan kowane alheri, yana daga hakan jin ƙan dabbobi da tausasawa garesu.

Hani daga musla ga mutum bayan kasheshi

Haramta dukkanin abin da a cikinsa akwai azabtarwa ga dabbobi.

التصنيفات

Yanka, Kyawawan Halaye