Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku

Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa waɗanda suke jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman Yana jin ƙan su da rahamarSa wacce ta yalwaci kowanne abu; don sakayyar da ta dace. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni da jin ƙan waɗanda ke ƙasa mutum ne, ko dabba, ko tsuntsu, ko waninsa na nau'ikan halitta sakamakon hakan (shi ne) Allah Zai ji kanku daga saman sammanSa.

فوائد الحديث

Addinin Musulunci addini ne na rahama, shi gabaɗayansa a tsaye yake a kan biyayya ga Allah da kyautatawa zuwa ga halitta.

Allah -Mai girma da ɗaukaka - Mai siffantuwa ne da rahama, kuma tsarki ya tabbatar maSa Shi ne Mai rahama a duniya Mai rahama a lahira, Mai sadar da rahama ne ga bayinSa.

Sakayya tana daga jinsin aiki, masu jin ƙai Allah Yana jin ƙansu.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Kyawawan Halaye