إعدادات العرض
Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi
Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Kurdî Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە Kiswahili پښتو অসমীয়া دری Malagasy or Čeština नेपाली Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు ไทย Српски മലയാളം Кыргызча Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Wolof Magyar ქართული Moore Українська Македонскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.فوائد الحديث
Cikar Musulunci ba ya kasancewa sai da rashin cutar da wasu ta kowanne bangare.
An kebance harshe da hannu da ambato; Dan yawan kura-kuransu da cutarsu, domin mafi girman sharruka suna bijirowa ne daga garesu.
Kwadaitarwa akan barin sabo, da lazimtar abinda - Allah Madaukakin sarki - Ya yi umarni da shi.
Mafificin musulmai shi ne wanda ya sauke haƙƙoƙin Allah - Madaukakin sarki - da haƙƙoƙin musulmai.
Yin ta'addanci yakan kasance da magana ko da aiki.
Cikakkiyar hijira ita ce kauracewa abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.