Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki

Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki

Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Bukhari ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a daya daga tafiye-tafiyensa sai ya yi alwala, lokacin da ya isa wanke kafafuwa sai Mugira dan Shu'uba - Allah Ya yarda dashi - ya mika hannayensa dan ya cire abinda ke saman kafar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na kuffi dan wanke kafafuwansa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka barsu kada ka cire su, ni na shigar da kafafuwamna a cikin kuffin alhali ni ina da tsarki (Alwala). Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shafa akan kuffinsa, maimakon wanke kafafuwa kenan.

فوائد الحديث

Halaccin shafa akan kuffi yana kasancewa ne a lokacin alwala na karamin kari, amma wanka dan babban kari (janaba, al’ada) babu makawa daga wanke kafafuwa.

shafa yana kasancewa ne sau daya da shudar da hannu mai danshi akan saman kuffin banda kasansa.

An shardanta shafa akan kuffi ya zama ya sanyasu bayan ya yi cikakkiyar alwala ya wanke kafafuwansa da ruwa, kuma kuffin ya zama mai tsarki, mai suturta bigiren farillar na kafa, kuma shafarsu ya zama a karamin kari ne ba a janaba ba ko abinda yake wajabta wanka ba, kuma shafar ta zama a kayyadajjen lokaci a shari'ance shi ne yini da dare ga mazaunin gari, matafiyi kuma kwana uku da dararensu.

Ana kiyasta dukkanin abinda yake suturta kafafuwa akan kuffi na jaurabi da wasunsu, to shafa akansu yana halatta.

Kyakkyawan dabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da koyarwarsa, inda ya hana Mugira ciresu, ya kuma bayyana masa dalili: Cewa shi ya shigar da su suna tsarki; dan ransa ya natsu, ya kuma san hukuncin.

التصنيفات

Ladabai da Hukunce Hukuncen Tafiya, Shafa a kan Huffi da waninsa