إعدادات العرض
1- Na kasance tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a wata tafiya,sai na sunkuyo don in cire masa huffi,sai yace: ka barsu don na shigar da kafafuna da tsarkinsu,sai yayi shafa akansu.
2- Bai dace ga mace ba tayi Imani da Allah da Ranar Lahira tayi Tafiyar wuni da Kwana ba tare da Maharramunta ba
3- "Idan Mutum Uku suka futa tafiya to su dora dayansu ya zama shugaba"
4- Cewa Lallai Annabi ya Kasance yana Tasbihi akan abin hawansa, kuma ko ina ya sanya fuskarsa, yana nuni da kansa, kuma haka ma Dan Umar yake yi
5- Tafiya yanki ne na Azaba
6- Annabi ya hana tafiya da Qur'ani zuwa garin Abokan Gaba
7- Manzon Allah ya kasance idan yayi tafiya yana neman tsarin Allah daga Wahalar Tafiya, da Mummunar Dawowa, da tabarbarewar Yanayi, da kuma Addu'ar wanda aka Zalunta, da kuma Mummunan gani a cikin Ahali da Dukiya"
8- "Mahayi shi Kadai Shaidan ne, Mahaya Biyu kuma Shadanu biyu ne, Guda uku kuma Karafka"
9- "Idan kukai tafiya a cikin Yalwa, to ku bawa Rakuma hakkinsu na Kasa, kuma idan kukai Tafiya cikin Fari kuyi Saurin Tafiya, kuyi gaggawar wanketa"
10- "Na Umarce ku da yin tafiya cikin duhun dare, Saboda Kasa ana Nade ta da daddare"
11- "Manzon Allah ya Kasance, yana jinkirtawa a bayan Matafiya, Saboda ya taimakawa Rarrauna, Kuma ya dauke shi kuma yayi Masa Addu'a"
12- "Ya ku Jama'ar Muhajirai da Mutanen Madina, Lallai cewa daga cikin ku akwai wasu Mutane basu da Dukiya, ko Dangi, saboda haka wani daga cikinku ya hadu da Biyu ko Uku"
13- Mun tafi mu taro Annabi SAW tare da Yara a Thaniyat Al-Wadaa