Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta

Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana haramta akan mace musilma ta yi tafiyar dare (daya) sai idan akwai namji muharraminta tare da ita.

فوائد الحديث

Ibn Hajar ya ce: Rashin tafiya ga mace ba tare da muharrami ba, shi ijam'i ne a wanin Hajji da Umarh, da fita daga kasar shirka, daga cikinsu (malamai akwai) wanda ya sanya hakan daga sharuɗɗan Hajji.

Cikar shari'ar musulunci, da kwaɗayinta akan kiyaye mace da kuma tsareta.

Imani da Allah da ranar lahira suna lazimtar da ƙanƙar da kai ga shari'ar Allah, da kuma tsayuwa a iyakokinta.

Muharramin mace shi ne mijinta ko wanda yake haramta a gareta (ta aure shi) har abada saboda 'yan uwantaka, ko shayarwa, ko sukurtaka, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce; domin cewa abin nufi daga muharrami (shi ne) tsare mace da kareta da tsayuwa da sha'aninta.

AlBaihaƙi ya ce game da riwayoyin da suka zo a tsawon tafiyar da mace ba za ta yi tafiya ba sai tare da muharrami: Abin tabbatarwa cewa dukkan abinda ake ambatansa tafiya to an hana mace daga gare shi ba tare da miji ko muharrami ba, daidai ne ya kasance kwana uku ne ko kwana biyu ko kwana ɗaya ko tafiyar wasu awanni ko wanin haka; saboda riwayar Ibnu Abbas abar wawaitawa (Mutlaka ce), ita ce kuma ƙarshen riwayoyin Muslim wacce ta gabata: (Kada mace ta yi tafiya sai tare da muharraminta) wannan yana haɗa dukkan abinda ake ambatansa tafiya. Ya tiƙe. Wannan hadisin ya kasance gwargwadan mai tambaya ne da kuma ƙasarsa.

التصنيفات

Ladabai da Hukunce Hukuncen Tafiya, Wajiban Umra