Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira

Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira

Daga AbdurRahman Dan Abu Laila cewa sun kasance a wajen Huzaifa, sai ya nemi a shayar, sai wani Bamajushe ya shayar da shi, lokacin da ya ajiye ƙwaryar a hannunsa sai ya jefe shi da ita, kuma ya ce: Da badan ni na hana shi ba, ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba - kamar cewa shi ya ce: Ban aikata wannan ba -, sai dai cewa ni na ji annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana maza sanya alhariri da dukkan nau'o'insa. Kuma ya hana maza da mata ci da sha a kofinan zinari da azirfa. Kuma ya bada labari cewa su na muminai ne a ranar lahira; domin su sun nisancesu a duniya dan biyayya ga Allah, Amma kafirai to ba su da rabonsu a lahira; domin su sun yi gaggawar daɗaɗasu a rayuwarsu ta duniya dan sun riƙesu, da kuma saɓawarsu ga umarnin Allah.

فوائد الحديث

Haramcin sanya alhariri da dibaji ga maza, da kuma narko mai tsanani akan wanda ya sanya shi.

An halastawa mata alhariri da dibaji.

Haramcin ci da sha a farantan zinari da azirfa da kuma kofunan su akan maza da mata.

Kausasawar Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - a inkari, kuma ya bayyana hakan da cewa shi ya hana shi ne sama da sau ɗaya daga amfani da zinari da azirfa, sai dai shi din bai hanu ba.

التصنيفات

Ladaban Tufafi