Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance

Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da zato; domin cewa zato shi ne mafi karyar zance, kada ku yi binciken (aibobin mutane), kada ku yi hassada, kada kujuyawa juna baya, kada ku yi kiyayya, ku zama bayin Allah 'yan uwa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani, yana gargadarwa daga sashin abinda yake kaiwa zuwa rabuwa da gaba a tsakanin musulmai, daga cikin hakan: (Zato) shi ne tuhumane da yake faruwa a cikin zuciya ba tare da wani dalili ba, ya kuma bayyana cewa shi ne mafi karyar zance. Da (Bincike): Shi ne bincike game al'aurorin mutane ta hanyar gani ne ko kasa kunne. Da (bincike): Shi ne bincike daga abinda ya boyu daga al'amura, mafi yawan abinda ake fada a (Tajassus) a sharri ne. Da kuma: Game da (hassada) ita ce kin samuar ni'ima ga wasu. Da kuma: (Juyawa juna baya) shi ne sashi ya bijirewa sashi, ba zai yi sallama ba, ba zai ziyarci dan'uwansa musulmi ba, Da kuma: (kiyayya da juna) kiyayya da gujewa, kamar cutar da wasu ne, da daure fuska da mummunar tarba. Sannan ya fadi wata kalma wacce ta tattaro halayen Musulmai sashinsu tare da sashi da za ta gyara su ita ce:(ku zama bayin Allah 'yan uwa). 'Yan uwantaka tana kulla alakoki dake tsakanin mutane, da suke haduwa da ita, kuma tana kara soyayya da sabawa a tsakaninsu.

فوائد الحديث

Mummunan zato ba ya cutar da wanda alamominsa suka bayyana daga gare shi, ya wajaba akan muminai su zama masu basira masu fahimta, kada su yaudaru da munanan mutane da kuma fasikai.

Abin nufi shi ne gargadarwa daga tuhumar da take zama a cikin zuciya, da kuma nacewa akanta, amma abinda yake bijirowa a cikin zuciya ba ya tabbata to wannan ba'a dorawa da shi.

Haramta sabubban kyamar juna da yankewa a tsakanin zamantakewar musulmai, na bincike da hassada da makancinsu.

Wasicci da yi wa musulmi mu'amala mu'amalar dan uwa, a nasiha da kauna.

التصنيفات

Munanan Halaye