Duk wanda ya fita neman ilimi to zai kasance a kan tafarkin Allah har sai ya dawo

Duk wanda ya fita neman ilimi to zai kasance a kan tafarkin Allah har sai ya dawo

Daga Anas - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Duk wanda ya fita neman ilimi to zai kasance a kan tafarkin Allah har sai ya dawo."

[Hasan ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Ma'anar hadisin: Wanda ya fita daga gidansa ko kasarsa Don neman ilimin shari'a, yana zuwa karkashin hukuncin wanda ya fita zuwa jihadi saboda Allah Madaukaki, don haka zai koma ga danginsa. Domin kamar mai gwagwarmaya ne wajen rayar da addini, da wulakanta Iblis, da wahalar da kai.

التصنيفات

Falalar Ilimi