إعدادات العرض
Addu'a ita ce ibada
Addu'a ita ce ibada
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].
[Ingantacce ne]
الترجمة
العربية తెలుగు हिन्दी Kurdî English Kiswahili Français فارسی தமிழ் සිංහල မြန်မာ Русский ไทย Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe Bosanski മലയാളം دری Fulfulde Magyar ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių or Română Kinyarwanda Српски O‘zbek Moore नेपाली Oromoo Wolof Български Українська Português Tagalog Azərbaycan ქართული тоҷикӣ Македонски bm 中文 Malagasyالشرح
Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa ga Allah, duka ɗaya ne, ta kasance addu'ar tambaya ce da nema, da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - abin da zai amfaneshi, da tunkuɗe abin da zai cutar da shi a duniya da lahira, ko addu'ar ibada, ita kuma itace dukkanin abin da Allah Yake sonsa kuma Ya yarda da shi na maganganu da ayyuka na zahiri da baɗini, ibadu na zuciya ko na jiki ko na dukiya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kafa dalili akan haka ta inda ya ce: Allah Ya ce: {Ku roƙeni zan amsa muku, lalle waɗanda suke girman kai game da bauta min, da sannu za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu}.فوائد الحديث
Addu'a ita ce asalin ibada, ba ya halatta a juyar da ita ga wanin Allah.
Addu'a ta ƙunshi haƙiƙanin bauta da iƙirari bisa wadatar Ubangiji da ikonsa - Maɗaukakin sarki -, da buƙatuwar bawa gareshi.
Narko mai tsanani sakamakon girman kai game da bautar Allah da barin roƙonsa, kuma waɗanda suke girman kai game da roƙon Allah za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu.
التصنيفات
Falalar Addu'a