Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan

Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan

Daga Sufyan Dan Abdullah AlSakafi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".

[Ingantacce ne]

الشرح

Sahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata magana mai tattaro ma'anonin Musulunci, da zai yi riko da ita, wacce ba zai tambayi waninsa game da ita ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: Na kadaita Allah, kuma na yi imani da cewa Shi ne Ubangijina kuma Allah na, Mahaliccina, Abin bautata na gaskiya ba Shi da abokin tarayya, Sannan ya jawu ga biyayya ga Allah ta hanyar bada farillan Allah, da barin abubuwan da Allah Ya haramta, ya kuma ci gaba akansu.

فوائد الحديث

Asalin Addini shi ne imani da Allah da UbangidantakarSa da AllantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.

Muhimmancin tabbatuwa bayan imani, da kuma ci gaba a cikin ibada, da tabbata akan hakan.

Imani sharadi ne na karbar ayyuka.

Imani da Allah, ya kunshi abinda kudire shi yake wajaba daga akidun imani da tushensu, da abinda yake bin hakan, daga ayyukan zuciyoyi, da jawuwa da mika wuya ga Allah a badini da zahiri.

Tabbatuwa lazimtar hanya ce, ta hanyar aikata wajibai da barin abubuwan da aka hana.

التصنيفات

Imani da Allah Maxaukaki, Tsarkake Zuciyoyi