Imani da Allah Maxaukaki

Imani da Allah Maxaukaki

12- Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "@Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci*, ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku, ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku, ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku, ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku, Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni, ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba, Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi, Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".

68- Mun kasance muna zaune a gefen manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, a tare damu akwai Abubakar, da Umar a cikin wasu mutane, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a tsakaninmu, sai ya ɗan jikirta mana, sai muka ji tsoron a cutar da shi ba mu sani ba, sai muka firgita, sai muka tashi, na kasance farkon wanda ya firgita, sai na fita ina neman manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har na zo wani shinge na mutanen Madina na Banu Najjar, sai na kewaye shi shin zan samu wata ƙofa gare shi ? ban samu ba, sai ga wata 'yar ƙorama tana shiga a cikin shingen daga rijiyar Kharija - rabi'u shi ne korama - sai na takure, sai na shiga wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi -, sai ya ce: "Abu Huraira" sai na ce: Eh, ya manzon Allah, ya ce: "Meke tafe da kai?" na ce: Ka kasance a tsakaninmu, sai ka miƙe, sai ka jinkirta gare mu, sai muka ji tsoron a cutar da kai bamu sani ba, sai muka firgita, sai na zama farkon wanda ya firgita, sai na zo wannan shingen, sai na takure kamar yadda dila yake takurewa, alhali waɗannan mutanen suna bayana, sai ya ce: "Ya Abu Huraira" sai ya bani takalmansa, ya ce: @"Ka tafi da takalman nan waɗannan, duk wanda ka gamu da shi ta bayan wannan shingen yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa tana sakankancewa da ita, to ka yi masa albishir da aljanna"*, sai Umar ya zama farkon wanda ya haɗu da ni, sai ya ce: Waɗannan takalman fa ya Abu Huraira? sai na ce: Waɗannan takalman manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya aikoni da su cewa wanda na haɗu da shi yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da ita, in yi masa albishir da aljanna, sai Umar ya daki tsakanin nonuwana da hannunsa sai na faɗi ta bayana, sai ya ce: Ka koma ya Abu Huraira, sai na koma wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai na fara shesseƙin kuka, kuma Umar ya hauni, sai gashi a bayana, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Meke damunka ya Abu Huraira?" na ce: Na hadu da Umar, sai na ba shi labarin abinda ka aikoni da shi, sai ya daki tsakanin nonuwana duka da na fadi ta bayana, ya ce: Ka koma, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Umar, me yasa ka aikata haka?" ya ce: Ya Manzon Allah, fansarka babana da babata, shin ka aiki Abu Huraira da takalmanka cewa idan ya gamu da wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da ita ya yi masa albishir da aljanna? ya ce: Eh, ya ce: Kada ka aikata, domin cewa ni ina jin tsoron mutane su dogara a kanta, kyalesu su yi aiki, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: to ka kyalesu.

79- Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, @Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.