Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku

Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku

Daga Abdurrahman ɗan Samura - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga rantsuwa da ɗawagitai, jam'ine na dagutu, sune gumakan da mushrikai suke bauta musu koma bayan Allah, sune sababin shisshiginsu da kafircinsu, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin hani daga rantsuwa da iyaye; inda ya kasance daga al'adar larabawa a Jahiliyya shi ne su yi rantsuwa da iyayensu dan alfahari da girmamawa.

فوائد الحديث

Rantsuwa bata halatta sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.

Haramcin rantsuwa da ɗawagitai, da kuma iyaye da shugabanni da gumaka, da abinda ke kama da su daga dukkan ƙarya.

Rantsuwa da wanin Allah yana daga ƙaramar shirka, takan iya zama shirka babba, idan akwai girmama wanda aka yi rantsuwa da shi a cikin zuciya, kuma shi yana girma shi kamar yadda yake girmama Allah, ko cewa shi yana ƙudirce wani abu a cikinsa na bauta.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya