Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka

Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka

Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Antambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga mafi girman zunubai sai ya ce: Mafi girmansu babbar shirka, ita ce ka sanya tamka ko kini ga Allah a AllantakarSa ko UbangidantakarSa ko sunayenSa da siffofinSa, wannan laifin Allah - Madaukakin sarki - ba ya gafartashi saida tuba, idan mai aikata shi ya mutu akansa to shi madawamine a cikin wuta. Sannan mutum ya kashe dansa dan tsoron ya ci tare da shi, kashe rai kuwa haramun ne, saidai zunubinsa yana girmama idan wanda aka kashe din yana da alaka ta jini da wanda ya yi kisan, kuma zunubinsa yana girmama yayin da manufar wanda ya yi kisan ta zama dan tsoron ya yi tarayya da wanda aka kashe din ne a arzzikin Allah. Sannan mutum ya yi zina da matar makocinsa shi ne ya yi kokarin rudar da matar makocinsa har ya yi zina da ita ta mika wuya gare shi . Zina haramun ce , saidai zunubinta yana girmama idan wacce aka yi zinar da ita matar makoci ce wanda shari'a ta yi wasicci da kyautatawa zuwa gareshi da yi masa kirki da kayauta zama da shi.

فوائد الحديث

Fifikon zunubai a girma, kamar yadda ayyuka na gari ma suna fifko a falala.

Mafi girman zunubai: Yi wa Allah - Madaukakkin sarki - shirka, sannan kashe da don tsoron ya ci tare da kai, sannan ka yi zina da matar makocinka.

Arziki yana hannun Allah tsarki ya tabbatar maSa, Ya yi lamuni da azurta ababen halitta.

Girman hakkin makwabci, kuma cutar da shi, shi ne mafi girman zunubi daga cutar da waninsa.

Mahalicci Shi ne macancanci ga bauta, Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya.

التصنيفات

Tauhidin Rububiyya, Tauhidin Rububiyya