إعدادات العرض
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල Kurdî Português മലയാളം తెలుగు မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Kiswahili தமிழ் دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Wolof Soomaali Moore Українська Български Azərbaycan mr ქართული тоҷикӣ bm Oromoo Македонскиالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan cewa ci gaba da zalunci da laifuka da shirka da zaluntar mutane a haƙƙoƙinsu, to, lalle Allah maɗaukaki Yana saurarawa azzalumi ya jinkirta masa, ya tsawaita masa a rayuwarsa da dukiyarsa ba zai gaggauta masa uƙuba ba, to, idan bai tuba ba sai ya damƙe shi, kuma ba zai sake shi ba, ba kuma zai ƙyale shi ba sabo da yawan zaluncinsa. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karanta: Kuma haka damƙar Ubangijinka take idan ya damƙi alƙaryu suna azzalumai, lalle damƙarsa mai raɗaɗi ce kuma mai tsanani ce.فوائد الحديث
Ya wajaba ga mai hankali ya yi gaggawar tuba, kuma kada ya lamuncewa kamun Allah, idan ya kasance wanda yake kan aikata zalunci.
Jinkirtawar da Allah Yake yi wa azzalumai da kuma rashin gaggauta yi musu uƙuba ɗaurin talala ne garesu, da kuma ninka musu azaba idan ba su tuba ba.
Zalunci yana cikin sabubban uƙubar Allah ga al’umma.
Idan Allah Ya halakar da gari, to, zai iya yiwuwa akwai mutanen ƙwarai a ciki, to, su waɗannan za’a tashe su a ranar Alkiyama a kan abin da suka mutu akan shi na kyakkyawan aiki, ba zai cutar da su ba dan wannan ukubar ta hada da su.