Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura)

Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura)

Daga Abu Hayyaj Al’asadi, ya ce: Aliyu Ɗan Abi Talib, ya ce da ni: Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura).

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana aika sahabbansa a kan kada su bar ((mutum-mutumi)) na wani abu da yake da rai aka gina shi ko ba gina shi aka yi ba, sai sun kawar da shi, sun shafe shi. Kuma kada su bar kabari wanda aka ɗaga shi sai sun daidaita shi da ƙasa, sun rushe ginin da aka yi, ko sun sanya shi a shafe kada ya daga a bayan kasa ɗagawa mai yawa, kawai ya ɗaga kamar ɗani guda.

فوائد الحديث

Haramcin suranta abubuwa masu rai, domin suna cikin hanyoyin shirka.

Shar’antuwar gusar da mummunan abu da hannu ga wanda yake da doka ko iko a kan haka.

Kwaɗayin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kan gusar da duk wasu alamomi na maguzanci na hotuna da mutum mutumi da gine gine a kan kaburbura.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya