Mafi girman Laifuffuka: yiwa Allah Shirka, da kuma amincewa Makircin Allah, da kuma yankewa daga Rahamar Allah, da kuma debe Haso daga Rahamar Allah

Mafi girman Laifuffuka: yiwa Allah Shirka, da kuma amincewa Makircin Allah, da kuma yankewa daga Rahamar Allah, da kuma debe Haso daga Rahamar Allah

Daga Abdullahi Dan Masud -Allah ya yarda da shi- daga Annabi ya ce: "Mafi girman Laifuffuka: yiwa Allah Shirka, da kuma amincewa Makircin Allah, da kuma yankewa daga Rahamar Allah, da kuma debe Haso daga Rahamar Allah"

[Isnadinsa ingantacce ne] [Abdurrazak Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi ya fada a cikin wannan Hadisin cewa wasu Zunubai suna daga cikin Manyan zunubai su ne: Cewa ka a Sanya abokin tarayya ga Allah cikin Rububiyyarsa ko bautarsa, kuma ya fara da shi ne; sabida cewa sune mafi girman zunubai, da kuma yanke kauna da debe haso daga Allah; domin hakan munana zato ne ga Allah da kuma Jahiltar yalwar rahamarsa, kuma da yana daga cikin talala ga bawa da ni'ama har sai ya kamashi da laifinsa bai shirya ba, kuma ba ana nufin bayyana baki dayan Manyan Zunubai ba ne cikin abinda aka ambata ba; domin Manyan zunubai suna da yawa, abin nufi bayanin mafi girmansu.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya