إعدادات العرض
Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai
Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai
Daga Nana A'isha da Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - sun ce: Lakacin da (wafati) ya saukar wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara yana rufe fuskarsa da wani mayafinsa, idan ya ji ya yi masa tsanani sai ya yaye shi daga fuskarsa, sai ya ce yana hakan: "Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai" yana gargaɗi game da abin da suka aikata.
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog বাংলা Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ Русский Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە ไทย دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली Malagasy Italiano or ಕನ್ನಡ Oromoo Română Soomaali Српски Wolof Українська Mooreالشرح
Nana A'isha da Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - suna ba mu labarin cewa lokacin da wafati ya halartowa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara sanya wani yanki na riga a kan fuskarsa, idan numfashi ya wuyata a gareshi saboda magagin mutuwa, sai ya gusar da shi daga fuskarsa, sai ya faɗa a wannan halin mai tsanani: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, ya koresu daga rahamarSa; domin su sun gina masallatai a kan kaburburan Annabawansu, da ba don haɗarin al'amarin ba da bai ambace shi a irin wannan lokacin ba, saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana al'ummarsa da kamanceceniya da wannan aikin; domin yana daga aikin Yahudawa da Nasara, kuma hanya ce da za ta kai zuwa ga shirka da Allah - mai girma da ɗaukaka.فوائد الحديث
Hani daga riƙon kaburburan Annabawa da salihai masallatan da za a dinga sallah a cikinsu; domin hakan hanya ce zuwa shirka.
Tsananin himmatuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da kulawarsa a kan Tauhidi, da kuma tsoronsa daga girmama kaburbura; domin hakan yana kai wa zuwa shirka.
Halaccin la'antar Yahudawa da Nasara, da wanda ya aikata irin aikinsu na gini a kan kaburbura da kuma rikonsu masallatai.
Gini a kan kaburbura yana daga dabi’un Yahudawa da Nasara, a cikin Hadisin akwai hani daga kamanceceniya da su.
Daga cikin riƙon kaburbura masallatai akwai yin sallah a wurinsu, da kuma zuwa garesu (wato kallonsu), ko da ba a gina masallaci ba.
التصنيفات
Tauhidin Uluhiyya