Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu

Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu

Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zama a kan kaburbura. Kamar yadda ya hana yin Sallah ana kallon kaburbura, ta yadda kabari zai kasance ta inda alƙiblar mai Sallah take, domin hakan hanya ce ta shirka.

فوائد الحديث

Hana yin sallah a maƙabartu, ko tsakanin kaburbura, ko ana kallon kaburbura, sai dai Sallar janaza kamar yadda hakan ya tabbata a Sunnah.

Hana yin Sallah ana kallon kaburbura don toshe ƙofar kaiwa ga shirka.

Musulunci ya hana wuce iyaka a kan kaburbura ya kuma hana wulaƙantasu, ba wuce iyaka, kuma ba wulaƙantawa.

Alfarmar Musulmi tana nan bayan rasuwarsa, saboda faɗin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Karya ƙashin mamaci kamar karya shi yana raye ne.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya, Saraxan Sallah