Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa

Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa

Daga Umar Ibnu Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kada ku wuce gona da iri wajen yabona, yadda Nasara suka maida Dan Maryam, ni kawai bawa ne, to ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana hani daga wuce gona da iri da kuma ketare iyakar shari'a a yabonsa da kuma siffanta shi da siffofin Allah - Madaukakin sarki - da kuma ayyukansa wadanda suka kebanta da shi, ko cewa shi yana sanin gaibu, ko a kira shi tare da Allah, kamar yadda Nasara suka aikata tare da Isa Dan Maryam - amincin Allah ya tabbata a gare shi -. Sannan ya bayyana cewa shi bawa ne daga bayin Allah, ya kuma yi umarni da mu fada game da shi: Bawan Allah kuma ManzonSa.

فوائد الحديث

Gargadarwa daga ketare iyakar shari'a a girmamawa da yabo; domin cewa hakan yana kaiwa zuwa ga shirka.

Abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi akan sa ya afku a cikin wannan al'ummar, sai wasu mutane suka wuce gona da iri a Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, wasu mutanen kuma a iyalan gidansa, wasu mutanen kuma a waliyyai, sai suka fada a cikin shirka.

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi bawan Allah ne; dan ya bayyana cewa shi bawa ne wanda yake bauta ga Allah, ba ya halatta a juyar masa da wani abu daga abinda Ubangiji Ya kebanta da shi.

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya siffanta kansa da cewa shi Manzon Allah ne abin aikowa daga wurin Allah to gasgata shi da binsa ya wajaba.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya