‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa

‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa

Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».

[قال النووي: حديث حسن] [رواه ابن ماجه والبيهقي وغيرهما]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Lallai Allah Ya yi wa al'ummarsa rangwame akan halaye uku: Na farko: Kuskure, shi ne abin da ya bijiro daga garesu ba tare da ganganci ba, kuma shi ne musulmi ya nufi wani abu da aikinsa sai aikin na sa ya dace da abin da bai yi nufi ba. Na biyu: Mantuwa, shi ne musulmi ya zama mai tina wani abu, saidai a lokacin aikata shi sai ya manta shi, to babu zunubi a kan hakan. Na uku: Tilastawa, za’a iya tilastawa bawa yin wani aikin da bai yi nufinsa ba tare da rashin ikonsa akan tunkuɗe tilastawar, a wannan lokacin zunubi ko ƙunci ba zai faɗa kansa ba. Tare da lura da cewa matashiyar hadisin a abin da ke tsakanin bawa da Ubangijinsa ne, a kan aikata abinda aka haramta, amma barin abin da aka yi umarni akan mantuwa to ba zai saraya ba, amma da ace wani laifi zai faru akan aikinsa to ba zai sarayar da wani haƙƙi na abin halitta ba, kamar yadda da ace zai yi kisa akan kuskure, ko ya lalata wata mota akan kuskure to wajibi ne ya biya.

فوائد الحديث

Yalwar rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarSa ga bayinSa inda ya ɗauke musu zunubi, idan saɓo ya bijiro daga garesu akan waɗan nan halayen uku.

Falalar Allah ga Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma al'ummarsa.

Ɗauke zunubi ba ya nufin ɗauke hukunci ko biya, misali wanda ya manta alwala, sai ya yi sallah yana mai zatan cewa shi yana da tsarki, to babu laifi a kansa da hakan, sai dai wajibi ne akansa ya yi alwala kuma ya sake sallar.

Babu makawa a cikin ɗauke laifi da tilastawa daga samuwar sharuɗɗa, misali mai tilastawar ya zama mai iko akan zartar da abin da ya yi barazana da shi.

التصنيفات

Imani da Allah Maxaukaki