إعدادات العرض
Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so
Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Tiếng Việt Kiswahili پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or Malagasy नेपाली Čeština Oromoo Română Nederlands Soomaali తెలుగు ไทย മലയാളം Српски Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Lietuviųالشرح
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya yi masa magana a kan wani al'amari nasa, sannan ya ce: "Allah Ya so kaima ka so", sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa inkarin wannan maganar, kuma ya nusar da shi cewa hada mashi'ar abin halitta akan mashi'ar Allah da Waw shirka ce karama, ba ya halatta ga musulmi ya furtata, sannan ya shiryar da shi magana ta gaskiya: "Allah Ya so Shi kadai", sai ya kadaita Allah a Son Sa, kada ya hada mashi'ar (ganin damar) wani akansa ta kowanne nau'i daga nau'o'in hadawa .فوائد الحديث
Hani game da fadin: Allah Ya so kaima ka so, da abinda ke kama da shi daga abinda a cikinsa akwai hada mashi'ar (ganin damar) bawa akan mashi'ar Allah da Waw; Domin hakan shirka ce karama.
Wajabcin hana abin ki.
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - hakika ya kiyaye janibin tauhidi, da toshe hanyoyin shirka.
A lokacin hana abin ki yana da kyau nunawa wanda ake kira canjin da ya halatta, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Hadawa tsakanin fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a wannan Hadisin: "Allah Ya so Shi kadai", da fadinsa a daya Hadisin: "Ka ce Allah Ya so sannan ka so" cewa fadin mutum: "Allah Ya so sannan ka so" ya halatta, sai dai fadinsa: "Allah Ya so Shi kadai" yafi.
Ya halatta ka ce : "Allah Ya so sannan ka so" sai dai abinda ya fi, fadin: "Allah Ya so Shi kadai".
التصنيفات
Tauhidin Uluhiyya