Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa

Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa

Daga Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi - Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'ikun rahama ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoton masu rayuka; Hakan cewa hoton abinda yake da rai: Saɓo ne mai muni, kuma a cikinsa akwai kamanceceniya da halittar Allah, kuma hanya ce daga hanyoyin shirka, wasu daga cikinsu hoton abinda ake bautawa ne koma bayan Allah. Amma sababin hanuwarsu daga (shiga) gidan da a cikinsa akwai kare: Saboda yadda yake yawan cin najasa, kuma sashinsu an ambace shi Shaiɗan; mala'iku kishiyotin shaiɗanu ne, saboda munin warin kare; mala'iku suna ƙin mummunan wari, kuma su (karnuka) an yi hani daga kiwonsu; sai aka yi wa mai riƙonsu ukuba da haramcin shigar mala'ikun rahama gidansa, da sallarsu a cikinsa, da nema masa gafara, da sa albarkarsu gare shi da kuma cikin gidansa, da tunkuɗewarsu cutar Shaiɗan daga gare shi .

فوائد الحديث

Haramcin riƙon kare sai dai karen farauta ko gadin dabbobi ko gona.

Riƙon hotuna suna daga al'amura munana waɗanda mala'iku suna guduwa daga garesu, kuma samunsu a guri sababi ne na haramcin rahama, kwatankwacin haka a kare.

Mala'ikun da ba sa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoto sune mala'ikun rahama, amma masu gadin (mutane) da wasunsu daga waɗanda suke da wani aiki kamar mala'ikan mutuwa to su suna shiga kowane gida.

Haramcin rataya hotonan masu rayuka a bangwaye da wasunsu.

AlKhaɗɗabi ya ce: Kaɗai mala'iku basa shiga gidan da a cikinsa akwai kare ko hoto daga abinda riƙonsa yana haramta na karnuka da hotuna, amma abinda ba haramun bane na karen farauta da gona da kiwo, da hoton da ake wulaƙantasu a shinfiɗu da matasai da wasunsu to shigar mala'iku ba ya haramtuwa saboda shi.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya