Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah

Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah

Daga Tarik Ɗan Ashyam al’Ashja’i, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi yana cewa: Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin wanda ya faɗa kuma ya shaida da bakinsa: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya kafircewa abin da ake bautawa da ba Allah ba, ya barranta da dukkanin addinai ban da Musulunci, to, haƙiƙka dukiyarsa da jininsa sun haramta a kan Musulmai, ba abin da muke da shi sai zahirin aikinsa, ba za a kwace dukiyarsa ba, ba za a zubar da jininsa ba, sai dai idan ya aikata wani laifi, ko ɓarna da za ta tabbatar da hakan a Hukunce Hukuncen Musulunci. Allah Shi ne Yake jiɓintar hisabinsa ranar Alƙiyama, idan ya yi da gaskiya a ba shi lada, idan kuma munafiki ne a yi masa azaba.

فوائد الحديث

Furta: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, da kuma ƙin yarda da duk abin da ake bautawa da ba Allah ba, sharaɗi ne na shiga Musulunci.

Ma’anar (Babu abin bautawa da cancanta sai Allah), shi ne kafircewa duk abin da ake bautawa da ba Allah ba, na gumaka da ƙaburbura da sauransu, da kuma kaɗaita Allah da bauta.

Wanda ya zo da Tauhidi, kuma ya lizimci dokokin Musulunci, to, wannan ya wajaba a kame daga gare shi, har sai wani abu da ya saɓawa hakan ya bayyana.

Alfarmar dukiyar Musulmi da jininsa da mutuncinsa sai da haƙƙi [na shari'a].

Hukunci a nan duniya a kan zahiri ne, a lahira kuma a kan niyya ne da manufofi.

التصنيفات

Tauhidin Uluhiyya