Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?

Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?

Daga Katada - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya zantar damu cewa wani mutum ya ce: Ya Annabin Allah ya za’a tashi kafiri akan fuskarsa? Ya ce: " Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?"Katada ya ce: Eh na rantse da buwayar Ubangijinmu.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya za'a tashi kafiri akan fuskarsa a ranar Alkiyama ?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce; Shin yanzu wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama mai iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa a ranar Alkiyama ba?! Allah Mai ikone akan dukkan komai.

فوائد الحديث

Wulakantar kafiri a ranar Alkiyama kuma zai yi tafiya akan fuskarsa.

التصنيفات

Imani da Ranar Lahira, Tauhidin Rububiyya, Tauhidin Sunaye da Siffofi