Imani da Ranar Lahira

Imani da Ranar Lahira

6- "Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama*, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".

7- "Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi* - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".

50- Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "@Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu*, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.

85- "Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? @Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba*, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim. Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -". Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi". sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".