Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi

Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi, kofunansa kamar taurarin sama ne, wanda ya sha daga gare shi ba zai yi kishirwa ba har abada".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa yana da wani tafki a ranar Alkiyama, tsawonsa tafiyar wata ne kuma fadinsama kamar haka ne. Kuma lallai cewa ruwansa ya fi nono tsananin fari. Kuma cewa kamshinsa mai dadi ne ya fi kamshin almiski. Kuma kofinansa tamkar taurarin sama ne a yawansu, Wanda ya sha daga tafkin da wadancan kofinan ba zai yi kishirwa ba har abada.

فوائد الحديث

Tafkin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - matattarar ruwa ne mai girma, muminai za su zo masa daga al'ummarsa a ranar lahira.

Samuwar ni'ima ga wanda zai sha daga tafkin ba zai yi kishirwa ba har abada.

التصنيفات

Imani da Ranar Lahira