إعدادات العرض
Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba
Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wani nama sai aka ɗaga masa zira'i, ya kasance yana ƙayatar da shi sai ya gutsira daga gare shi gutsira (ɗaya), sannan ya ce: "Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim. Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -". Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi". sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Español Kurdî Português සිංහල Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી Nederlands አማርኛ മലയാളം Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance tare da sahabbansa a wata liyafa ta abinci, sai aka kawo masa zira'in akuya kuma ya kasance shi ne mafi ƙayatarwar namanta gare shi , sai ya gutsiri wani gutsire da gefen haƙoransa sannan ya zantar da su, sai ya ce: Nine shugaban 'ya'yan Adam a ranar alƙiyama; hakan dan zantarwa da ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki -. Sannan ya ce: Shin kun san saboda me hakan? ya ce: Mutane za'a tarasu ranar alƙiyama a wata ƙasa mai faɗi madaidaiciya miƙaƙƙiya miƙewa ɗaya, waɗanda ke cikinta mai kira zai jiyar da su kuma mai kallo zai kewaye da su wani abu daga garesu ba zai ɓoyar masa ba; dan daidaituwar ƙasar a cikinta babu abinda wani zai ɓoyewa masu gani da shi, kuma gani zai zarce musu, yana nufin da ace mutum zai yi magana da mutum na ƙarshe zai ji su, ido kuma zai gansu, rana zata kusantowa halittu gwargwadan mil, kuma baƙin ciki da ɓacin rai zai riskesu abinda ba za su iya ɗauka ba kuma ba za su iya jurewa ba, sai su nemi tsira da ceto. Sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi wa masu imani ilhama cewa su zo wajen (annabi) Adam uban mutane, sai sū zo masa su ambaci falalarsa, wataƙila zai nema musu ceto a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, zasu ce masa: Kai ne Adam uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya sa mala'ikunSa sun yi maka sujjada, kuma Ya sanar da kai sunayen komai, kuma Ya yi busa a cikinka daga ranSa, sai ya yi hanzari sai ya ce: Lallai cewa Ubangijina Ya yi fushi a yau, fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, sannan ya ambaci kuskurensa, shi ne cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya hane shi cin bishiya sai ya ci, kuma zai ce: raina, shi ne wanda ya cancanci a nema masa ceto ku tafi zuwa wanina ku tafi zuwa Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu; sai su ce: Kai ne farkon Manzon da Allah Ya aiko shi zuwa mutanen ƙasa, kuma cewa Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, sai dai cewa shi zai yi hanzari: Cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, lallai cewa akwai wata mummunar addu'a da ya yi ta akan mutanensa, raina shi ne wanda ya cancaci a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Ibrahim. Sai su zowa (annabi) Ibarhim sai su ce: Kai ne badaɗayin Allah a cikin ƙasa, ka nema mana ceto zuwa Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai ya ce musu: Lallai cewa Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa yin irinsa ba kafinsa, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, kuma lallai haƙiƙa na kasance na yi ƙarya ƙarya uku; sune faɗinsa: Lallai ni mai rashin lafiya ne, da faɗinsa: Babbansu ne wannan ya aikata, da faɗinsa: Ga matarsa Saratu ki ba shi labarin cewa ni ɗan uwanki ne dan ya kuɓuta daga sharrinsa. Gaskiya cewa kalmomin uku kawai sun kasance ne a zunubin zance, sai dai yayin da surarsu suka kasance surar ƙarya sai ya ji tsoro daga garesu dan ƙanƙar da kai daga ceto; domin cewa wanda ya kasance mafi sanin Allah kuma mafi kusancin matsayi ya kasance mafi girman tsoro, sai ya ce: Raina shi ne wanda ya fi cancantar a nema masa haka, ku tafi zuwa wanina ku tafi zuwa Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda mu muke cikinsa?! sai ya ce: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushin da bai taɓa fushi irinsa ba kafinsa, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai cewa ni haƙiƙa na kashe wani mutum da ba'a umarce ni na kashe shi ba, raina shi ne wanda ya fi cancanta a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Isa ɗan Maryam. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: Kai (annabi) Isa kaine Manzon Allah, kuma kalmarSa da Ya jefata zuwa ga Nana Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfiɗar goyo alhali kana ƙarami, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai ya ce: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba ko sau ɗaya, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, bai ambaci wani zunubi ba, raina shi ne wanda ya fi cancantar a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Muhammad. Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce: Ya Muhammad Kai ne Manzon Allah kuma cikamakin Annabawa, haƙiƙa Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai in tafi sai in je ƙarƙashin al’Arshi, sai in faɗi ina mai sujjada ga Ubangijina - Mai girma da ɗaukaka -, sannan Ya yi mini buɗin wani abu na gode maSa da kyakkyawan yabonSa, bai yi taba buɗi ga wani a gabana ba kafin ni ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in ɗaga kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangijina, al'ummata ya Uabangijina, sai akarɓi cetansa. Sai ace masa: Ya Muhammad ka shigar da wanda babu hisabi a kansu daga al'ummarka ta ƙofar dama daga ƙofofin aljanna, kuma su abokanan tarayya ne a cikin koma bayan hakan na ƙofofi. Sannan ya ce: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai tsakanin sasanni biyu na ƙofa daga ƙofar aljanna, kamar tsakanin Makka da San'a'a ta Yamen ne, ko kamar tsakanin Makka da Busra ta Sham ne ita ce birnin Hauran.فوائد الحديث
Tawadu'in Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da yadda ya amsa gayyata, da cin (abin ci) tare da dukkan sahabbansa.
Fifita Annabinmu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan dukkan mutane.
AlƘali Iyad ya ce; An ce: Shugaba wanda ya wuce mutanensa kuma ake komawa zuwa gare shi acikin tsanani, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne shugabansu a duniya da lahira, kaɗai Ya keɓanci ranar alƙiyama ne dan ɗaukakar shugabanci a cikinta, da kuma miƙa wuyan gabaɗayansu gare shi, kuma saboda kasancewar (annabi) Adam da dukkan 'ya'yansa ƙarƙashin tutarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Hikima a cikin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi musu ilhamar tambayar (annabi) Adam, da waɗanda ke bayansa a farko, ba'ayi musu ilhamar tambayar Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, dan bayyanar da falalarsa, shi ne ƙarshe a ɗaukakar matsayi, da kuma cikar kusanci.
An shara'anta ga wanda yake son wata buƙata daga bawa ya gabatar da siffar abin tambaya da mafi kyan siffofinsa a gabansa; dan ya zama mafi kira ga amsawa.
Yana halatta ga wanda aka tambaya daga wani al'amarin da ba shi da iko a kansa ya yi hanzari da abinda za'a karɓa daga gare shi, an so a nunar ga wanda ake zatan cewa shi ne mafi iko akan hakan.
Bayanin tsoron tsayuwa (alƙiyama) da tsananin taron akan bayi a ranar alƙiyama.
Tawadu'in Annabi, inda suka ambaci abinda ya wuce daga gare su; dan cewa su koma bayan wannan matsayar ne.
Tabbatar da ceto mafi girma a ranar alƙiyama, hakan dan rabewa ne tsakanin halittu.
Tabbaatar da Wasila da matsayi abin yabo ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Godiya ga Allah - Maɗaukkain sarki - da yabo basa ƙarewa, saboda haka ne Allah Zai buɗewa ManzonSa a wannan matsayar na kyakkyawan yabo gare shi abinda bai taɓa buɗe shi ga wani kafinsa ba.
Bayanin cewa al'ummar (annabi) Muhammad ita ce mafificiyar al'ummu, to su suna da wasu keɓantattun abubuwa a cikin shiga aljanna, inda waɗanda basu da wani hisabi akansu zasu shiga daga wata keɓantacciyar ƙofa garesu, kuma zasu yi tarayya da mutane a ragowar ƙofofin.
التصنيفات
Rayuwar Lahira